Labarai
Wani hafsan sojin kasar nan ya karya cewar an boye daliban Dapchi a jihar Yobe
Wani hafsan sojin kasar nan ya musanta cewa ‘yan matan Sakandaren Dapchi da mayakan Boko-Haram suka sace a baya-bayan nan an boye su ne a wani yanki na jihar Yobe.
Hafsan sojin wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya shaidawa manema labarai cewa ikirarin da dan majalisa Goni Bukar ya yi cewa mayakan na Boko-haram sun boye ‘yan matan ne a jihar Yobe zance ne kawai maras tushe da ba shi da makama.
Ya ce indai da gaske dan majalisar ya ke, ya san inda ‘yan matan su ke, to ai yasan abin da yakamata ya yi a matsayinsa na dan majalisa ba wai zama zayyi a Abuja ya fitar da sanarwa ba.
Hafsan sojin ya kuma nuna takaicin sa matuka kan yadda ya ce, ‘yan siyasa ke zama a Abuja su yi ta fitar da sanarwa suna kushe namijin kokarin da rundunar sojin kasar nan ke yi.
A baya-bayan nan ne dai dan majalisa mai wakiltar mazabar Yunusari/Geidam a zauren majalisar wakilai Goni Bukar, ya bayyana cewa mayakan na Boko-Haram da suka sace ‘yan matan sun boye su ne a cikin jihar Yobe.