Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wani kamfani ya jefa uwar dashi cikin rudani

Published

on

Ga alama dai kamfanonin adashin ‘yan gata na zamani dake fitowa su yi ta karbar kudin mutane da sunan tsarin kasuwancin zuba dubu guda a baka goma, na cigaba da fuskantar tazgaro inda ake ta samun rugujewar su, bayan tattara mutane su sha su basulla.

A baya dai mun ga irin wannan tsari na kasuwancin gwaggwabar riba da dama wadanda su ke farawa da karfi, amma karshe su zama kumfar gishirin andiris lakwas sai ka ji shiru da an yi ihu daya sai  murya ta dushe.

Wasu daga ciki dai sai bayan sun dade su na karbar kudin mutane sai a tsayar ace basu da rajistar sec, wasu kuwa kudin ne ya ke karye mu su sai kaga an zo ana zance da karkata kai.

Allah ne yasan yawan mutanen da suka zuba kudi a irin wadannan wurare kudin na narkewa, ko kaga an zo an rabu dutse a hannun riga.

Kowa ya san Galaxy, wanda bayansa ne aka sami Dantata success, wanda har yanzu ba a rabu da bukar ba, sai kuma ga MGB ta fito wacce har yanzu ana ta fama wajen samun mafita.

kuma ana tsaka da haka daidai lokacin wani kamfanin mai suna STC AREWA YANA cashe, domin duk wanda ya ziyarci ofishin kamfanin zai ga tarin motoci masu dauke da tambarin kamfanin lamarin dake nuna cewar karan wannan kamfani ya kai tsaiko. to amma wane tudu wane gangare sai gashi kwastomomi sun fara kokawa da shi wannan kamfani na STC Arewa, har ma wata mata da ta ce uwar adashi ce ita amma kudin ta ya makale a STC ta ke rokon mahukunta su taimaka su karba ma ta kudinta, mijinta wanda shi ne ya yi mata zagi zuwa ga kamfanin ya ce, kudin sun makale kuma masu daukar dashi sun fara kufula.

 

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/01/UWAR-DASHI-A-.mp3?_=1

Itama uwar dashin tace babbar matslar ta shine gudun barewar sana ar ta ta dashi,dan tuni ma ta sayar da kayan dakin ta ta fara biyan masu zuciya a kusa,dan haka take rokon a taimaka mata.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/01/UWAR-DASHI-B.mp3?_=2

Akan wannan korafi Wakilinmu Aminu Abdu Bakanoma ya ziyarci ofishin na STC Arewa inda ya gana da wani kusa da bai aminta a nadi muryarsa ba sai dai ya amsa bayanin cewar, ai gajen hakuri mutane su ke yi domin su na kokarin biyan mutane mako-mako.

Wannan kusa ya ce cigaba da karbar sabbin shiga domin kammala biyan wadanda suka shigo. wani abu da shima ke tayar da hankalin mutane shi ne yadda abaya bakin ofishin ya ke cike da sabbin motoci amma yanzu abin ya sauya.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!