Connect with us

Labarai

Masu kwacen waya sun zo hannu -‘Yan sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi holin wasu matasa da ta kama su na amfani da baburin adaidaita sahu su na yiwa mutane kwacen waya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a yau Laraba yayin holin a shelkawata rundunar dake dake Bampa.

Daya daga cikin wadanda aka yi holin na su ya bayyanawa Wakilin mu Bashir Sharfadi ya bayyana yadda suke gudanar kwacen Da baburin Adaidata sahu su ke kwacen wayar daga Kabuga zuwa sabuwar Jami’ar Bayero inda su ke hawa baburin su uku, da sun ga mutum ya na tafiya a kafa sai s u fizge su tafi a guje.

Ya kuma kara da cewar,Duk wanda ya yi musu gardama su na zare makami ne sannan su kwace wayar.

Wanda ake zargin ya kuma ce mai baburin Adaidaita sahun bai san su na fita kwacen waya da baburin ba.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!