Labarai
Wannan ne karon farko da aka yi cushe a dokar Haraji – Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a kasar nan a Jam’iyyar Labour, Peter Obi kuma jigo a jam’iyyar ADC ya ce babu ƙasar da ke samun cigaban da take buƙata ta hanyar tatsar mutanenta kawai.
Obi ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya wallafa a shafukansa na sadarwa, inda ya ce ƙasashen da ya ziyarta, abin da ya fahimta shi ne suna gudanar da mulki ne ba tare da ɓoye-ɓoye ba.
Ya ƙara da cewa dole a bayyana yadda kowane haraji yake, “kamar yadda za a karɓa da amfaninsa wajen ciyar da ƙasa gaba. Idan ba a yi haka ba, zai zama kawai an haifar da ruɗani ne da ƙara wa ƴan ƙasar nauyi.” a cewar sa
A ƙarshe ya ce wannan ne karon farko da aka yi cushe a dokar haraji a Najeriya, “domin ita kanta majalisa ta tabbatar akwai sauyi a dokar, amma duk da haka an buƙaci ƴan ƙasar su fara biyan harajin”
You must be logged in to post a comment Login