Siyasa
Wasu daga cikin ayyukan da shugaban karamar hukumar Doguwa ya cimma a kwanaki 100

Shugaban karamar hukunar Doguwa Hon. Abdurrashid Rilwan Doguwa ya ce zai ci gaba da samar da ayyukan more rayuwa ga al’ummar karamar hukumar.
Hon. Abdulrashid Rilwan ya bayyana hakan ne a wani bangare na kaddamar da ayyukan da ya cimma cikin kwanaki 100 da shigarsa Office dan jagorantar yankin nasa.
Cikin kwanaki 100 da ya yi ya Kaddamar da ginin sabbin dakunan Karatu 10 masu dauki da Ofisoshi da gurin Ajiya kaya wato Store da kuma ajujuwa 2 kowannen su.
Haka zalika ya gudanar da gyaran Asibitin mazabar Falgore.
Sannan ya yi aikin gyaran bangaren haihuwa dake babban Asibitin garin Doguwa bisa sahalewar gwamna jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Sannan ya bude aikin gyaran cibiyar addinin musunci wato Islamic Center dake Bamako a yankin Gangare dake karamar hujumar ta Doguwa.
Kazalika Hon. Abdurrashid Rilwan Doguwa ya ce akwai ayyuka masu yawa da zai samar domin bunkasa yankin na Doguwa.
A domin haka ne yake neman hadin kan al’ummar karamar hukumar da su ci gaba da bashi hadinkan da ya kamata dan ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login