Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wasu fitattun ƴan Najeriya na yunƙurin hallaka ni – Shugaban EFCC, Bawa

Published

on

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) Abdurrashid Bawa, ya ce, wasu ƴan Najeriya na yawan turo masa da sakonnin barazanar kisa, tun bayan da aka naɗa shi a matsayin shugaban hukumar.

 

Mista Bawa ya bayyana hakan ne yayin zantawa da gidan talabijin na Channels, ta cikin shirin, ‘Sunrise Daily’.

 

Sai dai ya ce, wannan barazana ba za ta sanya ya dakatar da yaƙi da ya ke yi da masu ci da gumin al’ummar ƙasar nan ba.

 

‘‘Abin mamakin shine a kwanan nan wani fitaccen mutum a ƙasar nan da hukumar EFCC ba ta gudanar da bincike akan sa, amma sai gashi ya yi mini barazanar kisa’’ a cewar sa.

 

“Wannan shike nuna yadda matsalar cin hanci da rashawa ta samu wajen zama tsakanin al’ummar Najeriya’’ inji Abdurrashid Bawa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!