Connect with us

Labaran Kano

Wasu likitoci sun rasa rayukan su

Published

on

Wasu manyan likitoci biyu sun rasa rayukan su a wani hatsarin mota akan hanyar su ta dawowa Kano yayin da wani guda ya samu munanan raunuka a kansa da kuma kirjin sa.

Likitocin uku Abubakar Abdulkadir da Abdulrahim Salihu da Abdulhafiz Abubakar sun bar garin Nguru dake jihar Yobe ne a jiya Juma’a, inda suka samu hatsarin mota kilomota kadan kusa da garin Gumel na jihar Jigawa.

Da yake zantawa da tashar Freedom Rediyo, tsohon mataimakin shugaban kungiyar likitoci na kasa Dakta Adamu Alhassan, ya ce Dakta Abubakar Abdulkadir kafin rasuwar sa yana aiki ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano, sannan kuma likita ne na wucin gadi a cibiyar lafiya ta Gwamnatin tarayya dake Ngurun jihar Yobe.

Dakta Abubakar Abdulkadir ya bar mace daya da kuma yara, da ake sa ran binne gawar sa a jihar sa ta Kaduna a yau dinnan.

Tsohon mataimakin shugaban kungiyar likitoci na kasa ya kara da cewa, Dakta Abdulrahim Salihu wanda shima babban likitan kashi ne a cibiyar lafiya ta Gwamnatin tarayya dake Nguru ya rasu a yayin hadarin, inda kuma Dakta Abdulhafiz Abubakar ya samu munanan raunuka.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,762 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!