Connect with us

Kasuwanci

Wasu ‘yan kasuwar Sabon gari sun koka kan yunkurin Uba Zubairu

Published

on

Wasu ‘yan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwancin a filin parking na Muhammadu Abubakar Rimi wato Sabon Gari anan Kano, sun koka dangane da yunkurin tashin su da suka ce shugabannin kasuwar na kokarin yi.

‘Yan kasuwar dai sun ce shugabannin kasuwar karkashin Uba Zubairu Yakasai, ya aike da wani mutum rike da abar magana yana cewa su tashi daga kasuwar nan da mako daya.

Sun kuma shaidawa Freedom Rediyo cewar shakka babu za su fada cikin mawuyacin hali idan aka tashe su.

Alhaji Abba Muhammad na zaman daya daga cikin shugabannin leburorin da suke aiki a wajen, ya bayyana cewa kasancewar dayawa daga cikin su masu kananan karfi ne, idan har aka tashe su basu san inda za su zauna don gudanar da kasuwancin su ba.

Da yake jawabi, daraktan mulki na kasuwar Muhammad Bashir Abdul Durumin Iya, ya ce Gwamnatin jihar Kano ce ta bayar da umarnin tashin su don za tayi amfani da wajen.

‘Yan kasuwar sun bayyana mana kafar mu cewar, mutanen dake kasuwanci a wajen sun doshi sama da dubu uku.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!