Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

A wata ana haihuwar jarirai dubu daya a asibitin Murtala

Published

on

A kowanne wata ana haifar jarirai da suka kai dubu daya a wata a asibitin Murtala dake nan Kano.

Wata likitar yara a asibitin koyarwa na Aminu Kano Dr Zubaida Farouk Ladan ce ta bayyana haka lokacin  da take tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.

Dr Zubaida tace a duk rana ana iya haifar jarirai dari a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake birnin na Kano.

Ta kara da cewa daga cikin abubuwan da ya kamata a duba domin inganta lafiyar jarirai ya hada da tsaftace guraran da ake ajiye su bayan an haife su.

Hukumomi sun rufe asibitin Maita a Kano

Gwamnatin Kano ta tuhumi shugaban asibitin Rimingado

Dr Zubaida ta kara da cewa a yanzu asibitin na Murtala na da gadajen kwantar da jarirai guda sha shida ne idan ana bukatar hakan da zarar an haife su.

Tace akwai wata cuta da ke samun jarirai da an haife su wanda ya kamata a duba da zarar masu karbar haihuwa sun karfi haihuwar jarirai.

Dr Zubaida Faruk tace rashin kwararrun masu karbar haihuwa na taimakawa kwarai da gaske wajen tabbatar da wasu cututtuka na jarirai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!