Labarai
Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar Biliyan 30 bisa rushe shaguna
Wata babbar kotun tarayya ta umurci gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta ajiye naira biliyan 30 a cikin mako guda, biyo bayan wata kara da kungiyar amintattun masu shagunan Masallacin Idi da ‘yan kasuwa suka shigar a kanta.
A watan Satumbar data gabata ne kotu ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta biya diyyar ga masu shagunan Masallacin Idi saboda rusa musu kadarorin da aka yi ba bisa ka’ida ba.
idan za’a iya tunawa dai, Gwamnan Kano, Abba K Yusuf, bayan hawansa mulki a karshen watan Mayu, ya bayar da umarnin rusa shaguna, manyan kantuna da otal, inda ya dage cewa sun sabawa tsarin jihar.
Wasu daga cikin kadarorin da aka ruguje har da gine-gine masu hawa uku da ke dauke da shaguna casa’in a kan titinun jihar Kano da otal din Nasarawa GRA, da aka fi sani da Daula Hotel, wanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta sake ginawa a karkashin shirin hadin gwiwa da wani kamfani.
Gwamnatin Kano ta kuma ruguza wani gini a sansanin alhazai da gwamnatin da ta shude ta sayar wa wasu mutane da kuma shaguna da aka gina a sassan kofar Mata da filin masallachin Idi.
You must be logged in to post a comment Login