Labarai
WHO ta ja hankali kan cutar daji
Hukumar lafiya ta duniya ta bukaci gwamnatoci da su inganta cibiyoyin lafiya a kasashe masu tasowa da wadanda suka cigaba.
Hukumar lafiya ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta wallafawa a shafita a yayin da ake gudanar da bikin ranar cutar daji ta duniya da ake gudanarwa a duk ranar 4 ga watan Fabrairun kowacce shekara.
Hukumar ta WHO ta gargadi kasashe da cewar muddin ba’a shawo kan cutar daji ba, nan da dan lokaci zai karu da kimanin kaso 60 cikin dari.
Sanarwa ta kara da cewa za’a samu wannan kari na masu cutar ne da kaso 81 cikin dari a kasashe masu tasowa inda ko a yanzu wadanda suke dauke da cutar ke shan wahalar samun sauki daga cutar daji.
Mataimakin darakta a hukumar wanda yake kula da bangaren samar da lafiya da cutuka masu yaduwa da wadanda basa yaduwa Dr Ren Minghui ya ce wannan kididdiga yunkuri ne na zaburar da kasashe domin shawo kan matsalar cutar daji.
Inda ya ce da zarar an samarwa al’umma cibiyar lafiya da za’a dinga kai marasa lafiya , hakan zai taimaka wajen gano cutar da akan lokaci .