Labarai
INEC ta amince da David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta amince da jagorancin jam’iyyar ƴan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin shugabancin tsohon shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, David Mark
Hukumar zaɓen ta yi hakan ne bayan wallafa sunan shugabannin jam’iyyar a shafinta na intanet.
Hakan na zuwa ne bayan fafutikar da haɗakar ƴan’adawa na ƙasar ke yi wajen ganin sun yi abin da suka kira “inganta jam’iyyar” domin tunkarar babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.
A ranar 2 ga watan Yulin wannan shekara ne haɗakar ƴan hamayyar siyasa na Najeriya suka ayyana ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi amfani da ita, tare da bayyana Sanata David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da kuma sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Sai dai duk da haka an shafe tsawon lokaci babu sunan sabbin shugabannin da aka ayyana a shafin na hukumar Inec.
You must be logged in to post a comment Login