Connect with us

Labarai

Ya zama wajibi kamfanoni da ƴan kasuwa su riƙa biyan Haraji- Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta ce, ya zama wajibi kamfanoni da ƴan kasuwa su riƙa biyan kuɗaɗen haraji domin tabbatar da gwamnatin jihar ta samu kuɗaɗen da za ta samar wa da al’ummar ci gaba tare da samar da tsare-tsaren da suka kamata a cikin kasuwanni.

 

Shugaban hukumar tsara bayanai da taswirar Kano watau KANGIS Dakta Dalhatu Aliyu Sani ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabancin kasuwar hatsi ta Dawanau domin bayar da haɗin kai wajen biyan dukkanin haƙƙin gwamnati da yake kan ƴan kasuwa.

 

Dakta Dalhatu Sani ya ƙara da cewa zasu tabbatar sun zauna da dukkanin shugabannin kasuwannin dake jihar domin wayar musu da kai kan yadda zasu dunga biyan gwamnati hakkin ta.

 

Da yake jawabi shugaban kasuwar Hatsi ta Dawanau Alhaji Muttaka Isah, ya ce, za su tabbatar sun bayar da duk wata gudunmawa ga gwamnatin wajen wayarwa da ƴan kasuwar su ta Dawanau kai wajan biyan gwamnati haraji.

 

Shugaban hukumar ya kuma shawarci dukkanin ƴan kasuwa da kamfanoni masu zaman kansu da su kasance masu biyan gwamnati haraji yadda aka tsara domin ciyar da Kano gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!