Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

Yadda bikin ranar muhimmancin mallakar katin dan kasa ke gudana a Kano

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ware ranar sha shida ga watan Satumbar kowacce shekara a matsayin ranar shaidar katin dan kasa da nufin wayar da kan al umma irin muhimmancin da katin ke dashi ga kowanne dan kasa.

Ka zalika a nan Najeriya dai an fara gudanar da bikin ne a shekarar 2018, da nufin wayar da kan alumma kan muhimmacin mallakar katin dan kasa.

Najeriya dai na gaba gaba daga cikin jerin kasashen duniya da suke dauke da mutane masu yawa,kuma daga cikin al ummar kasar basa mayar da hankali wajan yin shaidar katin dan kasar.

Amma lura da cewa arewacin kasar nan al umma basa mayar da hankali wajan yin shaidar katin dan kasa duk kuwa da cewa it ace yankin da tafi yawan jama’a a Najeriya.

A wata kididdiga da hukumar samar da katin dan kasa ta fitar a shekarar da ta gabata da 2019 tace kaso ashirin cikin dari ne kadai sukai rijistar katin dan kasa a Najeriya.

A nan kano ma haka abun yake domin Hukumar dake samar da lambar katin dan kasa reshen jihar kano ta ce mutane miliyan biyu da dubu daya da talatin ne sukai rijistar katin zama dan kasa cikin mutane sama da miliyan Ashirin da suke jihar.

Jama’a da dama dai a kasar nan suna kokawa saboda fuskantar matsalar dangwala hannu da kuma rashin wadatattun shiyoyi mafi kusa da zasuje suyi bayaga cinkoso da ake samu da sauran matsaloli.

Shin ko mutane sun san muhimmancin katin dankasa da kuma dalilan bikin ranar?mun zanta da wasu mutane anan kano inda suka bayyana ra’ayoyin su.

“Sun ce wahalhalun da ake fuskanta shi ne ke sababa rashin zuwa don mallakar katin dan kasar ya yin da wasu ke cewa ba bu cibiyoyin yin katin dan kasar a kusa”.

Lawal Yahaya Shine shugaban hukumar yin rijistar shaidar katin dan kasa ta jihar kano ya bayyana irin alfanun da shaidar ke dashi.

“Ya ce idan zaka fita kasashen waje sai da katin dan kasar ya yin da nan gaba kadan idan za’a yi cinakayya a kasar nan”

Ya kuma ce ya kamata alumma su dinga yin rajistar shaidar katin dan kasa domin nan bada dadewa ba za’a magance duk wata matsala da ake fuskanta a baya.

Y ace saboda hakan ne ma ya sanya gwamnatin tarayya ta dauki gabaren wayar da kan al ummar ta irin muhimmancin da shaidar katin dan kasar ke dashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!