Labarai
Da gaske jami’an tsaro na aiki da “CCTV” a Kano?
A makon da ya gabata ne mai taimakawa gwamnan Kano kan kafafan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai ya fitar da wani bidiyo a shafinsa na Twitter, wanda ke nuna cibiyar sanya idanu kan halin da ake ciki a yankunan Kano ta hanyar amfani da kyamarar CCTV da gwamnatin Kano ta samar.
Despite Kano being the most peaceful State in Nig for the last 5yrs (Alhamdulillah), H.E @GovUmarGanduje is not relenting in his effort to further secure the state, as his admin has installed CCTV around the metropolis with a control centre at police HQ to be commissioned soon. pic.twitter.com/Fx3YPElqVC
— Peacock (@dawisu) September 7, 2020
A ranar Litinin ɗin nan ne wasu shafukan internet na jamhuriyyar Nijar suka fitar da wasu hotuna da bidiyo na yadda wasu matasa suka yiwa wata mata ƙwacen jaka ɗauke da wuƙa a birnin Niamey na jamhuriyyar.
Sai dai kuma, daga baya wasu cikin hadiman gwamnatin Kano sun wallafa waɗannan hotuna da cewar kyamarorin da aka sanya a Kano ne suka fara aiki.
Wannan batu dai ya jawo cece-kuce a kafafan sada zumunta, inda al’umma ke bayyana mabanbanta ra’ayoyi a kai.
Labarai masu alaka:
Akwai bukatar karin kungiyoyin tsaro a Kano
Ganduje zai mayar da dajin Falgore wurin atisayen sojoji
Freedom Radio ta tuntuɓi Adama Musa wata ƴar jarida a gidan rediyon Amfani da ke birnin Niamey wadda ta tabbatar mana da faruwar lamarin, inda ta ce, tuni jami’an tsaro suka cafke matasan da aka gani a cikin bidiyon.
Wata majiya mai tushe a rundunar ƴan sanda ta Kano ta tabbatarwa da Freedom Radio cewa, wannan hotunan da ake yaɗawa ba daga wurin su ya ke ba.
Majiyar ta tabbatar da cewa gwamnatin Kano ta samar wa da rundunar sabbin kayayyakin aiki na zamani ciki kuma har da kyamarorin na CCTV.
Wasu masu bibiyar al’amuran yau da kullum a Kano na cewar zai yi wuya tsarin amfani da CCTV ɗin ya ɗore cikin ƙanƙanin lokaci, musamman ganin yadda ko da fitilun titi ba su gama tsayawa da ƙafar su ba.
You must be logged in to post a comment Login