Labarai
Yadda aka yi wa gawar tsohon shugaban ƙasa Buhari faretin girmamawa

Dakarun Sojojin Najeriya bisa jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, sun gudanar da faretin girmamawa ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
An gudanar da faretin ne a filin jirgin sama na Umaru Yar’adu da ke garin Katsina, jim kaɗan bayan isar gawar daga birnin Landan.
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ne ya jagoranci dawo da gawar marigayin kamar yadda shugaba Tinubu ya ba shi Umarni.
Marigayi tsohon shugaban ƙasa Buhari ya rasu ne a Birtaniya ranar Lahadi da misalin karfe 4:30 na yamma kamar yadda makusantansa suka sanar.
You must be logged in to post a comment Login