Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda Ganduje ya kaddamar da sabunta rijistar APC a mazabar sa

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce domin tabbatar da cewa, an yi aikin sabunta rijistar Jamiyyar APC cikin tsari an kafa kwamitoci masu karfi domin kulawa da yadda ake rajistar.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi wannan bayani ne a jiya  ya yin da ya halarci garin Ganduje domin kaddamar da sabunta rijistar APC a mahaifar sa.

Gwamna Ganduje ya kara da kira ga Mata da su fitowa domin sabunta rajistar duba da cewa a lokacin zabe Mata na taka gagarumar gudunmawa wajen fitowa domin yin zabe.

Gwamna Ganduje ya ce, masu tsohuwar rijistar da aka yi tun  a shekara ta 2014 suma an basu dama don sabunta rajistar ta su.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa, ya yin kaddamar da yin rijistar magoya bayan jam’iyyar da dama ne suka  halacci wurin ya yin da uwar Jamiyyar ta  APC ta kasa turo Alhaji Kabiru Matazu  ya jagoranci kaddamar da yin rijistar.

Sauran wandanda suka halacci kaddamawar sun hada  da mataimakin gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna da sanatoci  da jagoran jam’iyyar APC ta Kano Abdullahi Abbas da ‘yan majalisa da sauransu masu ruwa da tsaki   na jam’iiyar anan Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!