Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda jana’izar Alhaji Sani Ɗangote ta kasance a Kano

Published

on

Ɗaruruwan al’ummar musulmi daga sassan Najeriya ne suka halarci jana’izar marigayi Alhaji Sani Dangote da safiyar ranar Laraba.

An jana’izar ne Alhaji Sani Dangote, ƙani ga Alhaji Aliko dangote a Ƙofar kudu da ke fadar sarkin Kano.

Jana’izar wadda liman Malam Sani Muhammad ya jagoranta, da misalin ƙarfe 10 na safe.

Cikin waɗanda suka halarci jana’izar sun haɗar shugaban majalisar dattijai sanata Ahmad Lawal da ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika da kuma gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sai mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ɗan uwan marigayin Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Abdussamad Isyaka Rabiu da gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum.

Sauran su ne: Sanata Ali Ndume da sanata Bukola Saraki sai Yusuf Magaji Bichi da sauran baƙi daga ciki da wajen ƙasar nan.

Tun da fari marigayin shi ne mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote kuma ya rasu a wani asibiti da ke ƙasar Amurka ranar Lahadi 14 ga watan Nuwambar 2021 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Kuma an binne gawarsa a maƙabartar Sarari, wadda anan ne ake binne iyalan Ɗantata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!