Labarai
Yadda muka gano ministar da ta sayi kaddarar dala miliyan 37 a ɓoye– Abdurrasheed Bawa
Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Abdurrasheed Bawa, ya bayyana yadda ya ce, hukumar ta gano yadda wata minista ta sayi kadara a ɓoye da kudin-ta, ta kai dala miliyan talatin da bakwai da dubu ɗari biyar.
A cewar shugaban hukumar ta EFCC matar har ta ba da kuɗin kafin alƙalami da ya kai dala miliyan ashirin.
Sai dai Abdurrasheed Bawa bai bayyana sunan ministar ko kuma bayyana karara cewa a wannan gwamnati ta rike mukamin ko kuma a gwamnatin baya ba.
Abdurrasheed Bawa ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da gidan talabijin na Channels, ta cikin shirin ‘Sunrise DAILY’.
Shugaban hukumar ta EFCC ya kuma ce, masu satar kuɗaɗen gwmanati suna amfani da ɓangaren sayan kaddarori ne wajen ɓoye kuɗaɗensu.
You must be logged in to post a comment Login