Connect with us

Labarai

Shugaba Buhari ya kai ziyarar duba ayyuka a jihar Borno

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a filin jirgin saman sojoji da ke Maiduguri a wata ziyarar aiki da ya kai jihar Borno.

Shugaban ya sauka a jihar ne da misalin karfe goma da minti biyar na safiyar yau Alhamis 17 ga watan Yuni.

Cikin wadannan suka tarbi shugaba Buhari har da gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum da yan majalisun tarayya da na jihohi da sauran mukarraban gwamnati.

Ana sa ran shugaba Buhari zai fara duba yadda ake gudanar da faretin bangirma kafin ya kai ga kaddamar da wasu ayyukan da za su inganta harkokin tsaro a rundunar Operation Hadin kai da ke Maimalari.

Idan dai za a iya tunawa tun a jiya Laraba ne 16 ga watan Yuni, shugaban hafsoshin tsaro na kasa janar Lucky Irabor da sufeton yan sandan kasar nan Usman Alkali Baba suka isa Maiduguri don kyautata tsaro kafin zuwan shugaba Buhari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!