Labarai
Yadda PDP ta yi taronta na kwamitin zartaswa karo na 100 duk da kutsen yan sanda

Bayan shafe tsawon yinin jiya Litinin ana kai ruwa rana tsakanin mambobin babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, jam’iyyar ta gudanar da taron na kwamitin zartaswa watau NEC karo na 100.
Taron na zuwa ne bayan wani zaman sirri da gwamnonin jam’iyyar suka gudanar a gidan gwamnatin jihar Bauchi da ke unguwar Asokoro a Abuja.
Shugaban jam’iyyar na riƙo, Ambasada Iliya Damgum, ya shai da wa manema labarai cewa, taron ya mayar da hankali kan abu guda ɗaya, koda ya ke bai bayyana batun ba.
Taron dai na zuwa ne bayan shafe tsawon yinin jiya Litinin ana dambarwa tsakanin mambobin kwamitin da jami’an ƴan sanda game da taron.
You must be logged in to post a comment Login