Labarai
Za’a fara electronic voting a Najeriya – Kabiru Gaya
Kwamitin zabe na majalisar dokokin dattawar kasar nan ya ce za su fito da tsari na gudanar da zabe a kasar nan ta hanyar na’ura wato electronic voting don rage magudi a Najeriya.
Shugaban kwamitin zaben na majalisar dattawan kasar nan sanata Kabiru Ibrahim Gaya ne ya bayyana hakan a jiya lokacin da yake ganawa da ‘Yan Jaridar fadar gwamnatin Kano.
Ya Kara da cewa zaben ta hanyar naura wato electronic voting zai taimaka Gaya wajen kawar da magudi tare da kawo tsari Mai tsafta a tafiyar da hukumar zabe.
Ya kuma ce daga abubuwan da kwamitin ke son kawo gyara ya hada da rage yawan jamiyyun zabe a kasar nan Wanda ake so su koma guda biyar
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa Sanata Kabiru Gaya ya Kuma yi kira ga ‘Yan takarar shugabancin kananan hukumomi da su bi dukkanin dokokin yin maslahar da aka yi a tsakanin su da kuma hada kai don yin zaben cikin lkwanciyar hankali da umana.
You must be logged in to post a comment Login