Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yajin aiki: Ƴan daba sun mamaye sakatariyar kungiyar NLC a Kaduna

Published

on

Ƴan daba dauke da muggan makamai sun mamaye harabar sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da ke Kaduna.

 

Rahotanni sun ce ƴan dabar wadanda yawansu ya haura ɗari sun isa sakatariyar ƙungiyar ce wanda anan ne wajen da ƴan ƙungiyar kwadago ke taruwa kafin fara zanga-zangar da suke yi wanda ɗaya ne daga cikin matakan da suke dauka na ci gaba da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da su ka fara.

 

Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa daga bisani ƴan sanda sun tarwatsa dandazon ƴan dabar tare da kama guda ashirin daga cikinsu.

 

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ASP Muhammad Jalinge ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa tuni aka tura da jami’an tsaro don dakile barkewar rikici

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!