Labarai
Yajin aikin ƴan sahu: Ganduje na yunƙurin ruguza tattalin arziƙin Kano – PDP
Jam’iyyar PDP mai adawa ta zargi gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da yunkurin ruguza harkokin tattalin arzikin jihar.
Hakan kuwa na zuwa ne, bisa ƙin sasantawa da matuka baburan adaidaita sahu da suka tsunduma yajin aiki tsawon kwanaki uku.
Cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi ya fitar a ranar Laraba ce ta zargi hakan.
A cewar sanarwar, Kano ta shahara da harkokin kasuwanci daban-daban na da kuma sufuri, sai dai rashin sasanta rikicin da ke tsakanin gwamnati da matuka baburan ya haifar da koma baya a bangaren tattalin arziki.
Jami’iyyar PDP ta kuma zargi cewa, gwamnatin Kano ta mayar da hukumar KAROTA wata babbar hukumar tara kuɗaɗen shiga maimakon ta zama hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda tsarinta yake.
Wannan dai na zuwa yayin da aka shiga rana ta uku da fara yajin aikin matuka baburan adaidaita sahu a Kano, lamarin da ya gurgunta al’amuran yau da kullum.
You must be logged in to post a comment Login