Connect with us

Labarai

‘Yan bindaga sun yi garkuwa da mutane a jihar Adamawa

Published

on

Wasu ‘yan bindiga da ba’a kai ga gano ko suwaye ba sun yi garkuwa da wasu mutane shida a jihar Adamawa.

Lamarin ya faru ne da tsakar ranar jiya Asabara a karamar hukumar Gurin, Fufore dake jihar ta Adamawa.

Wasu shaidun gani da ido a jihar sun shidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutanan ne a wani kauye dake cikin karamar hukumar ta Fufore-Gurin.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Adamawa ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai Magana da yawun rundunar DSP Suleiman Nguroje, inda ya ce mutun hudu ‘yan bindigar su ka samu nasarar garkuwar da su a kauyen.

Yayin da mutane biyu suka kubuta daga cikin mutane shida da yan bindigar suka kama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!