Connect with us

Labarai

Zulum- ya baiwa malamai 30 kwangilar addu’o’i a kasa mai tsarki

Published

on

Gwamnatin jihar Borno ta umarci manyan malamai guda talatin da su gudanar da addu’oin kan kungiyar mayakan Boko Haram da suka jima suna kawo tashe-tashen hankula a jihar.

Gwamnan jihar ta Borno Babagana Zulum ne ya bukaci hakan ta cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun gwamnan Isa Gusau ya fitar ga manema labarai.

Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya lashi takobin baiwa malaman guda talatin zuwa a kasar Saudi Arebiya da su gudanar da addu’oin kan rikicin na mayakan na Boko haram da ya dauki shekaru  yana gudana a jihar.

Isa Gusau ta cikin sanarwar ya kuma ce gwamnan jihar ta Borno ya kuma umarci malaman  dake zaune a kasar saudiyya da su dinga gudanar da dawafi a kowacce rana a ka’aba dan samun cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Borno dama kasar nan baki daya.

Ya kuma ce malamai talatin din dna zaune a kasar  Saudiyya da suka  fito  daga jihohin Borno da Katsina da Zamfara da kuma nan jihar Kano dama wasu sassan jihohin dake yankin Arewacin kasar nan.

Ya kuma ce malaman za su kasance ne a koda yaushe a bakin ka’aba suna rokawa jihar ta Borno da kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!