Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘yan sanda a jihar Bauchi sun kashe wasu ‘yan fashi

Published

on

‘Yan sandan jihar Bauchi sun kashe wasu yan fashi a yayin da suke aikin sintiri  a filin gidan mai dake jihar ta Bauchi .

Kakain rundunar yan sanda ta jihar Bauchi Kamal Abubukar ne ya bayyana wa manema labarai hakan a jiya litini, ya ce hakan ya faru ne biyo baya turo wasu sabbin yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya da kare dukiyar alummar da ke yankin

Ya ce kwamishinan yan sanda jihar Habu Sani , ya bayyana cewar ‘yan fashin sun yi yunkurin aikata fashi da makami a ranar 22 ga wannan wata , inda yace rundunar ta su ta samu wata wayar gaggawa yayin da ‘yan fashin su biyar  dauke da makamai da suka da Ak-47, tare da yiwa gidan man da ke kan titin Bauchi-Jos tsinke tare da kokarin yi musu sata.

Tuni rundunar yan sanda ta farwa barayi inda ta bude musu wuta , suka yi bata kashi, a yayin da suke tsaka da bude musu wutar ne aka sami daya daga cikin barayin yayin da saura suka tsere.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!