Connect with us

Labarai

Yan kasuwar sayar da wayoyi ta Unguwa Uku sun nemi daukin gwamnatin Kano

Published

on

Wasu daga Cikin yan kasuwar sayar da wayoyin hannu ta Unguwa Uku wato GSM Market sun koka akan yanda suke zargin shugabancin kasuwar da yi musu Mulkin Kama Karya harda Cin zarafin wasu daga cikin yan kasuwar.

A zantawar wasu daga cikin yan kasuwar da Freedom Radiyo sun ce, sun dade suna bukatar sauyin shugabancin a kasuwar  saboda rashin adalcin da ake nuna musu,

Har ma suka kara da cewa tsawon shekara sama da goma kenan shugaban kasuwar  yana kai kuma yaki bari ayi zabe, tare da hada kai da wani tsohon jami’in Dansanda har takai ga kotu ta aike da wasu daga Cikin yan kasuwar Gidan ajiya da Gyaran hali.

A nasa bangaren shugaban Kungiyar Kasuwar sayar da wayoyin hannu ta Unguwa Uku GSM Market Aliyu Abubakar Umar ya Magantu, inda yace wadanda akai kara kotu suna tada tarzoma ne acikin kasuwa hakan ce tasa aka hada su da hukuma har akayi musu Hukunci daidai da abinda suka aikata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!