Labarai
Yan Najeriya na da damar neman daukin kasashen waje kan matsalar tsaro – Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce ’yan Nijeriya na da cikakken ’yancin neman taimakon kasashen waje idan gwamnatin Nijeriya ta gaza kare rayukansu.
Obasanjo ya yi jawabin ne yayin wani taron Kirsimeti a Jos, inda ya ce bai kamata a ji kunyar neman taimako ba idan gwamnati ta kasa cika babban nauyinta na tsaro.
channels TV ta ruwaito Obasanjo ya ce a zamanin da ake amfani da tauraron dan adam da jiragen sintiri, bai kamata ’yan ta’adda su rika kashe mutane su bace ba. Ya zargi gwamnati da gazawa, yana mai cewa hare-hare da kashe-kashe sun yi yawa, kuma ’yan kasa sun gaji da zubar da jini.
Hakazalika, ya tuna da sace ’yan matan Chibok, yana mai cewa matsalar tsaro ta kara tabarbarewa maimakon ta inganta, kuma ya jaddada cewa kariyar ’yan kasa ita ce aikin farko na kowace gwamnati, amma a halin yanzu gwamnati ba ta iya kare al’umma yadda ya kamata ba
You must be logged in to post a comment Login