Connect with us

Labarai

Yan sanda a Zamfara sun kama mutum kan zargin mallakar kayan fashewa

Published

on

Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta sanar da kama wani mutum bisa zargin mallakar abubuwan fashewa ba bisa ƙa’ida ba, a wani samame da aka kai a ranar 27 ga Janairu, 2027.

Samamen ya gudana ne da misalin ƙarfe 4:15 na yamma, bayan samun sahihin bayanan sirri da suka jagoranci jami’an tsaro zuwa kai farmaki cikin nasara.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, “jami’anta na Task Force kan hana haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ƙarƙashin jagorancin ASP Aminu Aliyu ne suka kama wanda ake zargin mai suna Mustapha Mohammad mai shekaru 38.”

An kama shi ne yayin da yake tuƙin motar da binciken farko ya nuna cewa motar na ɗauke da abubuwan da ake zargin kayan fashewa ne 954 waɗanda aka ɓoye su a cikin buhunan robobi.

Rahotannin binciken sun nuna cewa ana zargin kayan an shirya amfani da su ne wajen ƙera ababen fashewa (IEDs) da ’yan bindiga ke amfani da su.

Rundunar ta ce “a halin yanzu wanda ake zargin yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da kayan da aka kama an adana su tare da miƙa su ga masu ƙwance abubuwan fashewa na rundunar domin ƙarin bincike da tantancewa.

Sanarwar ta ƙara da cewa bincike na ci gaba da gudana domin gano tushen kayan da inda aka nufa da su, da kuma gano sauran mutanen da ka iya kasancewa cikin wannan laifi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!