Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan sanda sun cafke sojoji kan KAROTA

Published

on

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Adullahi Haruna Kiyawa ya shedawa Freedom Radio cewa, sojoji uku na hannun su sakamakon wata hatsaniya da ta barke a tsakanin su da jami’an KAROTA da tsakar ranar jiya a kan kwanar Kasuwar Sharada dake karamar hukumar Birni da Kewaye a nan Kano.

Sojojin dai sun baiwa hammata iska a yayin da hatsaniyar ta barke a tsakanin su har ta kai ga an sami rauni.

Yadda rikicin ya samu asali:

Rahotanni dai sun bayyana cewa rikicin dai ya samo asali ne sakamakon aron hannu da ake zargin Sojojin sun yi don raste hanya, duk kuwa da cewa ba hannunsu bane, wanda kuma hakan ya sabawa doka, dalilin kenan da ya sanya ‘yan KAROTAR suka tare su.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana mana cewa ana tsaka da musayar yawu ne wani daga cikin sojojin ya doki dan karotar a ka har ya fasa masa kai.

An gurfanar da shugaban KAROTA a gaban Kotu

Hukumar KAROTA zata ware jami’an da zasu kula da cinkoson Safiya da dare

Jami’an KAROTA sun jikkata wasu matasa

Ko da muka tuntubi hukumar KAROTA don jin ko me hukumar za ta ce, jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka ma maganar tana hannun ‘yan sanda.

Haka zalika Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Adullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa runduna na cigaba da bincike bayan da aka yi zargin cewar sojojin na cikin Adai-daita Sahu al’amarin ya afko

Wakilinmu Umar Lawan Tofa ya rawaito cewa rikicin ya fara ne daga Kwanar Kasuwar Sharada har ta kai zuwa kan titin Yahaya Gusau.a nan Kano.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!