Labarai
An gurfanar da shugaban KAROTA a gaban Kotu
Babbar kotun jiha mai lamba 8 karkashin mai shari’a justice Usman Na’abba ta sanya ranar 14 ga watan gobe domin sauraran martani daga bakin wani lauya mai suna M.S Waziri a cikin kunshin wata kara wadda barrister Rabi’u Sa’idu Rijiyar lemo ya shigar.
Yana karar gwamnatin kano da shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Dan agundi.
Mai karar ta bakin lauyansa barrister Abubakar Sadik Usman ya roki kotun da ta tunbuke Baffa Babba Dan agundi daga shugabancin hukumar.
Hukumar KAROTA zata ware jami’an da zasu kula da cinkoson Safiya da dare
Jami’an KAROTA sun jikkata wasu matasa
Masu karar sun bayyanawa kotun cewar sashi na 11 sakin layi na 2 na dokar da ta kafa karota a shekarar 2012 ya zaiyano mutanen da suka cancanta su shugabanci hukumar kuma Baffan baya cikin wadanda suka cancanta.
Lauyan da yake Kare Baffa Barrister M.S. Waziri ya bayyana wa kotun cewar zai shigar da takardun suka akan ko kotun tana da hurumin jin karar, ko masu karar suna da hurumin shigar da karar.
Shima lauyan gwamnati Abubakar Sadik ya bayyana cewar zai shigar da takardun suka.
An kuma sanya 14 ga watan gobe dan jin martanin