Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan sanda sun cafke wani mutum da yayi barazanar yin garkuwa da uba da ɗa a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi da ake zarginsa da yunkurin garkuwa da wani Uba da ɗansa.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Litinin ɗin nan.

Haruna Kiyawa ya ce “wani mutum mazaunin ɗan Zabuwa da ke ƙaramar hukumar Bichi ya yi korafin cewa, wasu mutane sun kirashi a waya suna masa baranazar za su yi garkuwa da shi ko kuma ɗansa tun a ranar 1 ga watan 9”.

Kiyawa ya kuma ce “mutanen sun yi barazanar ya basu miliyan ɗaya ko kuma su yi garkuwa da ɗan sa idan ya tafi makaranta, ko kuma shi kan sa, lamarin da ya tayar da hankalin sa ya kira mu”.

DSP Kiyawa ya ce, tuni rundunar ta baza jami’an don gano inda mutumin mai suna Halliru Sa’adu ya ke, kuma an gano mutumin a jihar Nasarawa kuma anan yake bukatar a kai masa kudin.

Rundunar ta yi gargadi ga jama’a da su rika kai irin wannan koke da gaggawa don shawo kan lamarin, kasancewar mafi yawa daga masu yin barazanar a cikin yan uwa suke.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!