Labarai
‘Yan Sanda sun dakile yunkurin wani mummunan hari

Rundunar ‘yansanda a jihar Kogi ta ce jami’anta sun dakile wani yunkurin kai hari kan wani babban sansanin ‘yansanda a jihar da wasu yanta’adda suka yi, inda aka kama wasu da ake zargi da hannu cikin lamarin.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar a jihar William Aya ya fitar ga manema Labarai.
A cewar sa samun nasarar dakile harin ya biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu.
You must be logged in to post a comment Login