Connect with us

Labarai

‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Yobe

Published

on

‘Yan sandan Jihar Yobe sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da garkuwa da wani mutum bayan sun bayyana kansu a matsayin jami’an tsaro.

 

Hakan  na cikin sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a baya baya nan.

 

Sanarwar ta ce a ranar 16 ga Fabrairu 2026 da misalin karfe 10:30 na dare, jami’an ’yan sanda na ofishin Potiskum sun tare wata mota kirar Toyota Prado, inda suka ceto Abdulhamid Garba mai shekaru 35 daga Damaturu.

 

Bincike ya nuna cewa an sace shi ne a Damaturu bayan wadanda ake zargin sun yi karyar su jami’an tsaro  ne tare da zarginsa da laifin rashawa domin tsare shi da neman kudin fansa har naira miliyan 10 daga iyalan sa.

 

Rundunar ta ce an kama Mohammed Usman da Kabiru Ibrahim Umar da Idriss Abdullahi Zakaria da Matthew Obata, tare da kwato motar Toyota Prado da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin.

 

Sanarwar ta ce ana ci gaba da bincike domin gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kotu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!