Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Garkuwa da Mutane: ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargi da sace uwa da jaririyarta a Adamawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da kama mutane hudu da ake zargi da yin garkuwa da wata mata mai suna Hauwa Umaru da jaririyarta.

Mai magana da yawun rundunar DSP Sulaiman Nguroje ne ya sanar da hakan a Yola, inda ya ce mutanen da aka kama su ne suka kai hari ofishin ‘yan sanda na Nguroje a ranar 10 ga watan Oktoban 2021, dauke da manyan bindigogi.

DSP Sulaiman ya ce sun kama masu garkuwa da mutanen dauke da bindiga kirar AK-47 da tarin albusurusai, kuma suna cikin mutane bakwai da suka addabi Jihohin Adamawa da Taraba.

Ya kara da cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su gaban Kotu don hukunta su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!