Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan sanda sun kama wani Gurgu bisa zargin garkuwa da mutane a Katsina

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta cafke wani mutum mai larurar ƙafa, bisa zargin sa da hannu dumu-dumu wajen sace-sace da kuma yin garkuwa da mutane.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP. Gambo Isah, ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai a Katsina.

SP. Gambi Isah, yace gurgun ɗan asalin Kankiya mai suna Buhari Haruna, ɗan shekara 25, sun kama shi ne yayin da ya je karɓar kuɗin fansar da ya nema har miliyan biyu.

Tuni dai wanda ake zargin ya amsa laifin sa, yayin da rundunar ‘yansandan ke ci gaba da gudanar da bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!