Kaduna
Yan sanda sun kashe gawurtaccen ɗan fashi a hanyar Kaduna
‘Yan sandan Jihar Kaduna sun samu nasarar kashe wani gawurtaccen dan bindiga da ya addabi matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Mai magana da yawun rundunar ASP Muhammad Jalige ne ya tabbatarwa manema labarai hakan.
Jalige ya ce da asubahin jiya alhamis ne wasu mutane suka kira rundunar tare da sanar da ita cewa wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja,daidai kan wata gada da ke Kauyen Kasarami, suna harbin matafiya.
Daga nan ne jami’an na su suka durfafi wurin inda suka yi musayar wuta da su har suka fatatttake su, bayan da suka harbe guda daga cikinsu, sai dai wani direban mota da yaron motar sun rasa ransu a yayin fafatawar.
Jalige ya ce sun mika gawar direban da yaron motar zuwa asibitin St Gerald da ke Kakuri.
Sannan ya shawarci mazauna yankin da su ci gaba da ankarar da jami’an tsaro da zarar sun ga irin haka ta faru domin kai agajin gaggawa.
You must be logged in to post a comment Login