Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan sanda sun saki Nastura

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta saki shugaban hadakar kungiyoyin rajin kare Arewa, Nastura Ashir Sharif, a ranar Alhamis.

A ranar Talata ne ‘yan sanda suka cafke Nastura a Katsina, bayan ya jagoranci zanga-zangar lumana kan kisan da ‘yan bindiga ke yiwa wadanda basu ji ba basu gani ba.

Jim kadan da cafke shi ne kuma, ‘yan sandan suka tafi da shi birnin tarayya Abuja.

Wata sanarwa da kakakin kungiyar Abdul-Azeez Sulaiman ya fitar ya ce da yammacin ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sako shugaban nasu.

Haka zalika fitaccen dan gwagwarmayar nan Ibrahim Garba Wala ya wallafa hotansu da Nastura Ashir din da suka dauka a shalkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Abuja a shafin Facebook, bayan an sako shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!