Connect with us

Labarai

Yan ta’adda sun nemi a basu tarar dabbobi sama da 1500 a Katsina

Published

on

Gwamnan Jihar Katsina  Dikko Radda ya buƙaci al’umma su kwantar da hankalinsu, yayin da rahotanni ke cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun bai wa wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Kankia wa’adin kwanaki shida su bayar da shanu 700 da tumaki 1,000 a matsayin haraji.

 

Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa barazanar ta jefa jama’a cikin fargaba, inda da dama suka tsere daga gidajensu zuwa garuruwa kamar wasu sassan Jihar Kano. sama da kauyuka kusan goma ne suka yi hijira yayin da ake zargin wani jagoran ‘yan bindiga mai suna Muhammadu da jagorantar lamarin.

 

Sai dai daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Maiwada Dammalla, ya ce har yanzu gwamnati ba ta tabbatar da sahihancin wasiƙar ba, yana mai cewa ana zargin an ƙirƙire ta ne domin tayar da hankalin jama’a. Duk da haka, al’umma na ci gaba da fuskantar fargaba sakamakon rashin tsaro a yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!