Labarai
Ya na da kyau ‘yan jaridu su samar da shirin kan zaman lafiya- Sarki Kano
Mai martabar Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci masu yada labarai a gidajen jaridu dana ma’aikatun gwamnati da su ware wani shiri na musamman da zai rinka wayar da kan al’ummar Nijeriya kan muhimmancin da zaman lafiya yake dashi.
Sarkin na Kano ya bayyana hakan ne ta bakin Katukan Kano, Alhaji Habibu Bello Dankadai, yayin taron shekara da zaban sababbun shugabannin cibiyar kwararru kan hurda da Jama’a ta Nigerian Institute Of Public Relation (NIPR) da reshen Kano ta yi.
Alhaji Habibu Bello Dankadai ya Kuma ja kunnan sababbun shugabannin da aka zaba da su fito da hanyoyi na musamman da za su kara inganta aikin Jarida.
Da yake Jawabi sabon shugaban cibiyar ta hurda da jama’a reshen jihar Kano Aliyu Yusuf cewa ya yi, za su hada kan jami’an gwamnati dake ma’aikatu da manyan makarantu da Kuma na kafafen yada labarai wajen zuwa ayi tafiya a tare ta yarda za a kara ciyar da aikin yada labarai gaba.
A nasa jawabin gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da kwamishinan yada Labarai Baba Halilu Dantiye ya wakilta cewa ya yi, ‘gwamnati za ta ci gaba da taimakawa cibiyar ta NIPR wajen inganta harkokin yada labarai’.
Farfesa Abdallah Uba Adamu Malami a sashin koyar da aikin Jarida na Jami’ar Bayero dake Kano Wanda ya gabatar da takardar mai taken Kirkirarriyar Fasahar yada Labarai a fannin hurda da Jama’a Alfahunta da Kuma Kalubalanta a wani bangare na taron
Yayin taron dai an zabi Aliyu Yusuf a matsayin shugaba sai Isma’ila Ammai Maizare a matsayin mataimaki yayin da Abdullahi D. Abdullahi ya zama ma’aji sai Usman Gwadabe da ya kasance Sakatare da
Muhammad Dahiru Idris a matsayin mataimakin Sakatare ita kuwa Samira Sulaiman an zabe ta a matsayin Jami’ar hurda da jama’a ne sai Abdullahi Abba Hassan da ya kasance sakataren kudi da Ado Sa’idu Warawa a matsayin mai binciken kudi.
Rahoton: Abubakar Tijjani Rabiu
You must be logged in to post a comment Login