Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Yanzu haka PDP ta yi rashin ‘yan Majalisun dokoki 10 a Kano

Published

on

A ranar Juma’a 06 ga Mayun da muke ciki ne Mambobin Majalisar dokokin jihar Kano na
jami’iyyar PDP 10 suka sauya sheka zuwa NNPP mai alamar kayan marmari.

Tinda fari dai mambobin majalisar 9 ne suka fitar da sanarwar ficewa daga jami’iyyar zuwa NNPP.

‘Yan majalisar dokokin na Kano sun mika takardar fitar su ne ga shugaban majalisar Hamisu Ibrahim Chidari.

Sulaiman Yusuf Babangida Dawo-Dawo wai wakiltar Gwale ne dai ya zama kari cikin mambobin da suka sanar da ficewarsu.

Jumulla Mambobi 10 da suka sauya shekarar daga PDP zuwa NNPP sun hada da….

1.Rt Hon. Isyaku Ali Danja da ke wakiltar karamar hukumar Gezawa.

2.Hon. Umar Musa Gama mai wakiltar Nassarawa.

3. Hon Aminu Sa’adu Ungogo daga Ungogo.

4. Hon Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa Dala.

5. Hon. Tukur Muhd Fagge.

6. Hon.Mu’azzam El-Yakub, Dawakin Kudu.

7..Hon. Garba Shehu Fammar Kubiya.

8.. Hon. Abubakar Uba Galadima Bebeji.

9. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki, Kumbotso.

10- Hon Sulaiman Babangida Dawo-Dawo, Gwale.

Sanarwar hakan na zuwa ne bayan da Daraktan yada labarai na majalisar Uba Abdullahi ya fitar kuma aka rabawa manama labarai a makon da muke shirin bankwana da shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!