Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Kwankwaso da Shekarau sun shiga ganawar sirri

Published

on

An shiga ganawar sirri tsakanin tsohon Gwamna Kwankwaso da Sanata Malam Ibrahim Shekarau yanzu haka a gidansa da ke Munduɓawa.

Kwankwaso ya ziyarci Shekarau tare da muƙarrabansa da kuma ƴan jam’iyyar NNPP.

Kafin shiga tattaunawar sai da Kwankwaso da Shekarau suka gabatar da jawabai na nuna sun haɗu waje guda.

Daga bisani Malam Shekarau ya sanar da cewa za su yi ganawar sirri.

Magoya bayan tsoffin Gwamnonin biyu sun cika maƙil a gidan yayin da ake shirin taron karɓar Shekarau a NNPP gobe Laraba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!