Labarai
Yanzu-yanzu: Mahaifiyar A.A. Zaura ta shaƙi iskar ƴanci

Mahaifiyar dan takarar sanata a Kano Abdulsalam Abdulkarim Zaura ta shaki iskar ƴanci.
Shugaban karamar hukumar Ungoggo Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya tabbatar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Cikin harshen turanci ya ce”Alhamdulillah Hajiya Laure mahaifiyar A.A Zaura da aka yi garkuwa da ita ta kubuta cikin ƙoshin lafiya”.
A daren ranar Litinin ne wasu masu garkuwa da mutane suka sace Hajiya Laure mai shekaru sama 80 a garin Zaura a ƙaramar hukumar Ungoggo.
You must be logged in to post a comment Login