Connect with us

Labarai

Mahaifiyar Siasia ta shaki iskar ‘yanci

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tabbatar da kubutar da mahaifiyar tsohon mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samson Siasia Misis Beauty Ogere Siasia.

Masu garkuwa da mutane  suka  yi garkuwa da mahaifiyar tsohon mai horaswar tun kimanin makwanni 10 da suka gabata.

Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Asinim Butswat, ne ya tabbatar da sakin nata yana mai cewa za su yi cikakken bayani dangane da lamarin a nan gaba kadan.

Misis Beauty Ogere, mai shekaru 80 an  kubutar da ita ne da safiyar yau Lahadi, kuma  wannan shi ne  karo na biyu da ta fuskanci irin wannan matsala ta masu garkuwa da mutane.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!