Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu –yanzu : ‘Yan majalisar Kano suka shiga ganawar sirri da Ganduje

Published

on

A halin da ake ciki bayan sun kai ziyarar gaisuwar sallah ga gwamnan Kano ‘yan majalisar dokoki ta Kano sun kuma shiga ganawar sirri.

Da yammacin yau ne tawagar majalisar Dokokin jihar Kano karkashin jagorancin shugaban majalisar Abdulaziz Garba Gafasa suka kawo ziyarar gaisuwar Sallah ga gwamnan Kano.

Kakakin majalisar dokokin Abdulaziz Garba Gafasa ya ce sun kawo ziyarar ne domin yin gaisuwar Sallah ga gwamnan na Kano tare da godiya bisa ga yadda kyakkyawar dangantaka ke wanzuwa tsakanin majalisar dokokin da gwamnati.

Abdulaziz Gafasa ya Kara da cewa za kuma su cigaba da iyakar kokarin su wajen ganin ana cigaba da samun kyakkyawar dangantaka tsakanin majalisar da kuma gwamnati.

Da yake jawabi yayin karbar Yan majalisun Gwamnan na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana jin dadin sa bisa ga ziyarar inda yace abu ne mai kyau yadda dangantaka ke yin kyau a tsakanin su.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cew, ‘yan majalisar sun kuma shiga ganawar sirri da gwamnan na Kano bayan kammala jawabin gaishe-gaishe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!