Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

‘yar shekara 18 ta kashe jaririnta kwana guda da haihuwa a Jigawa

Published

on

Rundunar yan sandan a jihar Jigawa sun kama wata uwa mai shekaru goma sha takwas wanda basu bayyana sunanta ba da zargin kashe jaririnta da ta haifa, kwana guda da haifarsa sannan suka boye gawarsa a karamar hukumar Ringim.

Kakakin rundunar yan sandan SP Abdu Jinjiri ya bayyanawa kamfanin dillanci Najeriya hakan a garin Dutse dake jihar Jigawa.

Jinjiri ya bayyana cewa sun kama  matar mazauniyar kauyen Dandabi bayan da ta hada baki da kishiyar mahaifiyarta wajen aikata wannan al’amari, sannan suka binne jaririn da aka haifar ta haramtaciyyar hanya.

Tun da farko dai wasu mutane ne da suka samu labarin haihuwar da yarinya ta yi , bayan wani lokaci kuma suka nemi jaririn suka rasa wanda hakan ce ta sa suka kai kara.

Bayan faruwar hakan ne rundunar yan sanda ta fara bincikar lamarin inda aka kama yarinya bayan gudanar da bincike ne kuma aka tabbatar da cewa bayan cikin ya cika wata takwas ne aka dauke ta zuwa wani asibiti dake kauyen Sanka ta kuma haihu a can a ranar 31 ga watan Junairun wannan shekara da taimakon kishiyar mahaifiyarta.

Kuma sun kashe jaririn ne kwana guda bayan an haife shi,wato ranar 1 ga watan Fabrairun wannan shekara, suka kuma binne shi a wani daji.

Tuni dai yan sanda suka gano gawar wannan yaro aka kuma kai shi asibiti domin gudanar da bincike.

Ayayin da ake bincikar wanda ake tuhuma ne suka amince da kashe wannan jariri ta hanyar hanyar murde masa wuya, tare da binne shi da taimakon kishiyar mahaifiyarta.

Ana zargin wanda yayi mata ciki dan shekara 20 da haihuwa shima dan   garin Ringim tuni ya shiga hannu hukuma.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!