Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ana tafka kurakurai wajen amfani da Internet- kungiyar Smart Clicks

Published

on

Wata kungiyar mai rajin wayar da kan jama’a kan yadda za su yi amfani da shafin Intanet ta kyakkyawar hanya mai suna Smart clicks and initiate for Safer digital tools use, ta ce yadda mutane ke amfani da intanet a wannan lokaci akwai kura-kurai sosai

Shugabar kungiyar Suliyat Adeleye ldris ce ta bayyana hakan yayin taron Tadakar da yara yan makaranta yadda za su yi amfani da intanet din, don tunawa da wannan rana ta wayar da kan mutane kan yadda za su yi amfani da shafukan Intanet, da ake gudanarwa a yau.

Suliyat Adeleye ta ce yanzu amfani da intanet ya zama wani bangare na rayuwar mutane, inda ta ja hankalin jama’a cewa su kaucewa yada ko wane irin bayani a intranet.

Kano: INEC ta raba kayayyakin zaben ranar Asabar

Wasu daga cikin daliban da suka halarci taron sun bayyana farin cikinsu, tare da bayyana irin hanyoyin da za su bi don amfani da shafukan yadda ya kamata.

Wakilinmu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa a shekarar da ta gabata ne hukumar kula da kamtanin/sadarwa ta kasa NCC ta fitar da wani rahoto dake nuna cewa akalla yan Najeriya millyan dari da ashirin da biyu ne ke amfani da Intanet a ko wace rana.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!