Labarai
Yau ake sa ran dawowar Asiwaju Bola Tinubu daga Faransa
- A yau ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Nijeriya
- Hakan na zuwa ne kwanakin kadan kafin cikar wa’adin ranar rantsuwa da za a yi masa.
A yau ne ake sa ran sabon zababben shugaban Nigeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan shafe makwanni a kasar Faransa.
Daraktan harkokin kafafen yada labarai da hulda da jama’a na zababen shugaban kasar Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan, cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter da safiyar yau Litinin.
Dawowar tasa na zuwa ne kwanakin kadan kafin cikar wa’adin ranar rantsuwa da za a yi masa a ranar 29 ga watan Mayu mai kamawa.
Tun a ranar 21 ga watan Maris din da ta gabata ne zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya bar Najeriya zuwa kasar Faransa domin hutawa, kwanakin kadan bayan kammala zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris din.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login