Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ina cikin koshin lafiya kuma a shirye nake wajen karbar mulki- Tinubu

Published

on

Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar da cewa, yana cikin koshin lafiya, kuma a shirye yaki ya jagoranci Nijeriya yadda ya kamata.

Hakan ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa cewar Sabon zababben shugaban ba shi da cikakkiyar lafiya, dalilin kenan da ya sanya shi zuwa wasu kasashen duniya bayan bayyana sakamakon zaben da aka gudanar.

Cikin wata sanarwar da Tunde Rahman ya sanya wa hannu ya ce, zababben shugaban kasa Bola Tinubu, ya fita zuwa kasar Faransa da London da kuma Saudi Arebia inda ya gudanar da aikin Umrah, domin ya huta bayan kammala hidimar zabe.

A don haka sanarwar ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ake yada wa cewar Bola Tinubu ba shi da lafiya, wadda labarin bashi da tushe ballantana makama.

Da yammacin jiya Litinin ne Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya tare da mai dakinsa Oluremi Tinubu, inda suka samu tarba daga magoya bayansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!